The Daqing Oil Field, formerly romanized as "Taching", is the largest oil field in the People's Republic of China, located between the Songhua river and Nen River in Heilongjiang province.

Kamfanin mai na kasa NNPC ya bayyana cewa a watan Maris din shekarar 2023 zai fara gudanar da aikin hakar danyen man fetur a karon farko a Jihar Nasarawa.

Shugaban Kamfanin na NNPC Mele Kyari ne ya tabbatar da hakan a ranar Juma’a a yayin wata ziyara da gwamnan Jihar ta Nasarawa tare da wata tawagar daga Jihar su ka kai masa Ofishin sa.

Kamfanin na NNPC ya gano rijiyar man ta Keana ta yamma ne da ke Jihar ta Nasarawa na zuwa ne kasa da watanni biyar bayan kanfanin ya fara gudanar da hakar man a rijiyar Kolmani da ke tsakanin Jihohin Bauchi da Gombe.

Ta cikin sanarwar da kamfanin ya fitar a ranar Juma’a ya ce ayyukan da kamfanin ya ke ci gaba da gudanar na gano rijiyoyin Man Fetur a yankunan Tsandauri na Najeriya.

Shugaban Kamfanin ya ce sakamakon binciken da su ka gudanar sun gano akwai man fetur a cikin yankin.

Mele Kyari ya kara da cewa bayan gano rijiya za a fara gaggauta aikin sakamakon lokaci na sauyawa a duniya.

Kyari ya ce shekaru goma masu zuwa ba lallai ne kowa ya yadda ya zuba jarinsa a harkar man na fetur matukar ba yasan zai ci riba ba.

Inda ya bayyana cewa hakan ne zai sanya su fara aikin hakar danyen man da wuri.

Leave a Reply

%d bloggers like this: