A gobe Litinin shugaban kasa Muhammad Buhari zai tafi kasar Larabawa ta Mauritani domin halartar taron shugabannin kasashen Africa kan zaman lafiya.

Mai magana da yawun shugaba Buhari na Musamman Femi Adesina ne ya bayyana hakan a yau Lahadi.

Adesina ya ce taron da shugaban zai halarta shine karo na uku da fara gudanar wa.

A yayin taron shugaba Buhari zai gudanar da jawabi dangane da nasarorin da aka samu samuwar zaman lafiya a Africa.

Adesina ya kara da cewa a gurin taron za a bai wa shugaban Lambar girmama wa mai karfafa zaman lafiya a Africa wanda cibiyar da ke Abu Dhabi za ta bashi.

Adesina ya ce za a shugaban Lambar ne sakamakon jagorancin da ya nuna dangane da samar da zaman lafiya a nahiyar gudunmuwa da sulhu da ya taimaka dahi.

Bayan halartar taron shugaban zai dawo gida Najeriya a ranar Laraba,inda zai samu rakiyar ministan harkokin waje,ministan tsaro, Babagana munguno da sauran jami’an gwamnati.

Leave a Reply

%d bloggers like this: