Gwamnatin jihar Kano ta gurrfanar da wasu alƙalai da wasu miutane a gaban kotu bayan zargin badaƙalar naira miliyan 500.

Hukumar karɓar ƙorafe-ƙorafe da hana cin hanci da rashawa ta jihar Kano ce ta karɓi ƙorafin tare da bincike a kai.

An aike da alaƙalan da wasu mutane zuwa gidan ajiya da gyaran hali har zuwa 1 ga watan Fabrairun shekarar 2023 da mu ke ciki.

Da farko dai an gurfanar da alƙalan a gaban mai shari’a Mustapha Sa’id Datti wanda ya bayyana tuhumar da ake musu ta haɗa da manyan laifuka,  ciki har da sata da zagon ƙasa.

Laifukan da ake zargin mutanen da alƙalan su ka haɗa baki sun saɓa da sashe na 97, 79, 315 da sashe na 289 na kundin manyan laifuka.

Yayin zaman kotun a jiya Laraba, kotun ta yi watsi da buƙatyar wasu lauyoyi na bayar da belin wasu da ake tuhuma duk da hujjoji da su ka gabatarwa kotun.

A binciken hukumar hana cin hanci da rashawa ta jihar Kano ta gano kuɗaɗe, da wani asusun banki da aka yi amfani da shi wajen tura kuɗaɗen, da manyan sarƙoƙi, ababen hawa da wasu manyan kadarori da ake zargi an yi amfani da wasu wajen aikata zamba

Leave a Reply

%d bloggers like this: