Kamfanin mai a Najeriya ya ce ya ciri kuɗi naira tirliyan 3.3 domin biyan tallafin man fetur daga watan Janairu zuwa watan Disamba shekarar da ta gabata.

Kamfanin ya ce an ciri kuɗin ne daga asusun gwamnatin tarayya wanda kamfanin ya tara a matsayin haraji.

Hakan na ƙunshe cikin wani rahoto da kwamitin asusun gwamnatin tarayya ya gabatar ranar Talata.

Sai dai ana zargin gwamnatin Najeriya za ta dakatar da biyan tallafin man fetur a watan Afrilun shekarar da mu ke ciki.

Tun a shekarar da ta gabata wahalar man fetur ta fara tsanani wanda hakan ya sa wasu gidajen man ke siyar da shi a kan kuɗi da ya haura farashin gwamnati.

Duk da cewa an fara siyar da man fetur a shekarar 2022 a kan farashin lita guda naira 165, sai dai ya koma 185 a sirrance.

Kuma duk da hakan gidajen mai da dama na siyar da man a sama da farashin 185 da gwamnatin ta amince wanda hakan ke jawo dogayen layi da tsaiko a gidajen mai da dama.

 

Leave a Reply

%d bloggers like this: