Rundunar ƴan sanda a jihar Legas ta tabbatar da kama mutanen da ake zargi da aikata fashi da makami su 405 yayin da su ka samu damar hallaka 51.

Jami’an sun ce sun kama mutanen ne tsakanin shekarar 2021 zuwa shekarar 2022 da ta gabata.
Mai magana da yawun ƴan sandan jihar Benjamin Hundeyin ne ya bayyana haka yayin ganawa da kamfanin dillancin labarai na ƙsa NAN a jihar.

Ya ce sun samu damar kashe 25 yayin da su ka kama 245 a shekarar 2021, sannan su ka kama 160 tare da kashe 26 a shekarar 2022.

Wannan ke nuni da cewar an samu ƙarancin kama masu aikata fashi da makami la’akari da shekarar 2021.
Ya ƙara da cewa mutanen da aka kama sun samu nasarar ne bayan bibiya tare da fakon masu laifin.
Sannan akwai sauran masu aikata laifi daban-daban da aka kama kama daga kisan kai, garkuwa da mutane da kuma satar ababen hawa.