Yan makonni kafin babban zaben 2023, yan takarkar kujerar gwamna a jihar Kano sun sanya hannu a kan yarjejeniyar zaman lafiya.

Sanya hannun da yan takarar suka yi, ya biyo bayan gayyatar da kwamitin tabbatar da zaman lafiya ta jihar Kano wato KPC da hadin gwiwar Cibiyar Majalisar Dinkin Duniya da Kwamitin Zaman Lafiya na Kasa suka yi masu.


Sun rattaba hannun ne a wajen wani taron fadakar da yan takara kan muhimmancin zaman lafiya kafin, lokaci da kuma bayan zabe wanda aka yi a ranar Laraba, 18 ga watan Janairu.
Kwamitin ya kuma nusar da matasa da ke amfani da kafafen sadarwar zamani da su zamo masu yada abubuwan da zai amfani al’umma da wanzar da zaman lafiya a fadin kasar.
Yan takarar da suka sanya hannu kan wannan yarjejeniya ta zaman lafiya sun hada da Salihu Tanko Yakasai na Jam’iyar PRP, Sha’aban Ibrahim Sharada na Jam’iyar ADP da Injiniya Abba Kabir Yusuf wanda aka fi sani da Abba Gida-gida na Jam’iyar NNPP.
Sauran sune mataimakin dan takarar gwamna na Jam’iyar APC, Murtala Sule Garo, Bashir I. Bashir na Jam’iyar LP, Muhammad Abacha na Jam’iyar PDP, Mallam Ibrahim Khalil na Jam’iyyar ADC ya wakilce sa, sai kuma Bala Gwagwarwa na Jam’iyar SDP.
Giovanie Biha, wakiliyar Majilisar Dinkin Duniya ta Afirka ta ja hankalin yan takarar da su tabbatar da an gudanar da zabe a cikin kwanciyar hankali da lumana.