Shugaban kasar Najeriya Muhammadu Buhari, ya ce ya ɗauki alƙawari tun a baya cewa zai bauta wa Najeriya da mutanen da ke cikinta iyakar karfinsa.

Shugaba Buhari ya sake yin wannan furucin ne yayin da ya kai ziyarar gaisuwa ga Sarkin Bauchi, Alhaji Rilwanu Adamu, a wani ɓangare na yakin neman zaben ɗan takarar shugaban kasa na APC Bola Ahmed Tinubu a jihar Bauchi.
Shugaban ya ce a 2003 da 2012 ya kai ziyara baki ɗaya kananan hukumomi 774 da ke ƙasar nan.

sannan a shekarar 2019 lokacin da ya ke neman tazarce ya samu ikon zuwa kananan hukumomin jihohin Najeriya.

Shugaban ƙasan wanda ya nuna jin daɗinsa da irin tarbar da aka masa a fadar Sarkin, ya yabawa gwamna Bala Muhammed bisa ayyukan alherin da ya zuba wa al’umma a Bauchi.
Da yake jawabi, Sarkin Bauchi ya miƙa godiyarsa ga shugaban kasa bisa ziyarar da ya kai masa sannan ya roki ‘yan siyasa da su yi siyasa babu gaba.
Yayin da yake yaba wa Ƙauran Bauchi bisa baiwa kowace jam’iyyar siyasa dama a Bauchi, Basaraken ya yi wa shugaban kasa Addu’ar Allah ya sauke shi lafiya.