Wasu Mahara a Jihar Imo sun cire kan wani shugaban karamar hukumar Ideato ta Arewa Chris Ohizu da ke Jihar bayan sun yi garkuwa dashi.

Jaridar Punch ta rawaito cewa mahara sun yi aika-aikar ne a ranar Lahadi bayan karbar kudin fansa miliyan shida.
Wata majiya daga Jihar ta bayyana cewa bayan hallaka shi da maharan su ka yi sun yada faifan bidiyo akan kafar sadarwa ta zamani ta cikin wayar mamacin.

Majiyar ta ce kafin yanke masa kan sai da su ka fara daure shi daga bisani su ka cire masa kai.

Mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan Jihar Henry Okoye ya tabbatar da faruwar lamarin.
Kakakin ya ce rundunar ta na ci gaba da gudanar da bincike akan fariwal lamarin.