Gwamnatin jihar Kano da malaman addini daga bangarorin Izala, Qadiriyyah da Tijjaniyyah, sun bukaci gwamnatin tarayya da ta tsawaita wa’adin da babban Bankin kasa CBN ya sanya na daina karbar Tsoffin kudade.

Sun bukaci a tsawaita wa’adin daina karbar kudin ne, sakamakon rashin wadatuwar sababbin kudaden da aka canza wadanda jama’a zasu cigaba da amfani dasu.
Kiran ya biyo bayan wani zaman tattaunawa da aka yi, Wanda Gwanan Jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje da mataimakinsa Nasiru Yusuf Gawuna da sauran malaman suka halarta a Gidan Gwamnatin Jihar.

Idan za’a iya tunawa dai Babban Bankin ya tsayar da ranar 31 ga watan Janairu, a matsayin ranar karshe da za”a daina karba da kuma amfani da tsoffin kudin.

A wata takarda da jami’in yada labaran mataimakin Gwamnan Hassan Musa Fagge ya fitar, yace harkokin kasuwanci sun durkushe a Kano da Arewacin Najeriya, sakamakon karancin sababbin kudaden.
Sannan kuma a taron an yi kira ga Shugaba Buhari, da ya duba halin kuncin da Al’umma suka shiga a sakamakon hakan, sannan kuma a kara wa’adin daina karbar tsoffin kudaden.