Shugaban kasa Muhammadu Buhari yace, ya kalubalanci manyan kasar nan saboda tsawon shekarun da suka dauka suna nuna son kai a lamuransu, basa yunkurin kawo kawo cigaba a kasar nan.

Buhari ya fadi hakan ne a Gidan gwamnatin Jihar Katsina a Katsina, yayin wata liyafar cin abincin rana da gwamnatin Jihar ta shirya Dan karrama shi.
Shugaban yana ziyarar aiki ta kwana biyu a Jihar, ya shafe ranar farko yana zaga sako da lungu na kwaryar birnin Jihar, da kuma bude wasu ayyuka da gwamantin Aminu Masari ta samar a Jihar.

Buhari ya bayyana abinda ya kira a matsayin son kai na wasu ‘yan Najeriyar, inda yace da sunyi tunani sosai da an samu cigaba a kasar.

Sannan yayi takaicin dukiyar da aka lalata a maimakon alkintawa dan samar da abubuwan more rayuwa a gwamnatocin da suka gabata.
Ya kuma bayyana cewa, Manyan Najeriya basu hada Kansu Dan cigaban kasar ba a shekarun da suka gabata, sun kasance masu son kai, shi yasa na nace cewa suyi tunanin cigaban kasar fiya da kawunansu.
Yayin da yake magana akan titin jirgin kasa daga Katsina zuwa Maradin kasar Nijar, yace kowacce kasa sai ta hada kai da makwaftan ta Dan amfanar juna.