Ofishin babban bankin Najeriya CBN dake jihar Katsina ya fitar da sabbin kudi N120 million ga wakilan bankuna a jihar. Wannan ya biyo bayan ziyarar shugaba Muhammadu Buhari jihar inda ya kaddamar da wasu ayyukan da gwamnatin jihar ta kammala.

Bankin ya ce an yi hakan ne domin saukakewa mutane masu kudi kasa da Naira dubu goma sauya tsaffin kudadensu zuwa sabbi yayin wa’adin ranar 31 ga Junairu, 2023 ya matso.
Diraktan harkokin kudi na CBN, Ahmed Bello Umar, wanda ke jihar Katsina domin ganin yadda lamarin ke gudana a ranar Asabar ya ce bankin ya tura jami’ansa bibiyan yadda ake raba kudaden.

Ya yi bayanin cewa aikin wadannan jami’ai ya hada da bibiyan na’urorin ATM don tabbatar da cewa akwai kudade cikin don mutane su cira.

A cewarsa, ATM za ta baiwa mutane damar cire kudi.
Umar ya yi kira ga mutane su shigar da karan duk bankin da yaki budewa ko kuma bai bada sabbin kudi wajen CBN don a hukuntasu.