Hukumar zabe mai zaman kanta ta INEC ta tsawaita wa’adin daina karbar katin zabe na dindindin zuwa ranar 5 ga watan Fabrairun 2023.

 

INEC ta tsayar da ranar 31 ga watan Janairu matsayin ranar da za a daina karbar katin zaben dindindin amma kwamishinan hukumar, Festus Okoye yace an tsawaita tare da kara wa’adin don baiwa ‘yan Najeriya damar karbar katikansu.

 

Ya ce matakin ya biyo bayan taron da hukumar zabe ta INEC ta yi.

 

Okoye ya ce a cikin wata sanarwa a yau Asabar, dangane da rahotanni daga Jihohi daban-daban da tattaunawa da kwamishinonin zabe na mazauni, Hukumar ta yanke shawarar kara tsawaita karbar PVC a daukacin kananan hukumomin ta a fadin kasar nan da karin mako guda.

 

Don haka za a ci gaba da tattara na’urorin PVC a duk fadin kasar nan kuma za su kare a ranar 5 ga Fabrairun 2023.

 

Wannan dai shi ne karo na biyu da hukumar ke tsawaita karbar katin a fadin kasar kuma wannan shi ne karo na karshe na atisayen. An kara tsawaita lokacin tattarawa da karin sa’o’i biyu kuma za a fara da karfe 9 na safe kuma za a kare da karfe 5 na yamma a kullum ciki har da Asabar da Lahadi.

Leave a Reply

%d bloggers like this: