Shugaba Muhammadu Buhari ya yi kira da yan Najeriya su kwantar da hankulansu game da lamarin sauya fasalin Naira da kuma wa’adin daina amfani da tsaffin takardun Naira.

 

Buhari ya ce zai tabbatar da cewa al’umma da kasuwancinsu basu wahala ba kuma kowa zai samu sabbin kudi cikin ‘kankanin lokaci.

 

Buhari ya bayyana hakan yayin martani kan wahalan da yan Najeriya ke yi wajen layi a bankuna don mayar da tsaffin kudadensu.

 

Hakan ya biyo bayan jawabin dan takarar kujerar shugaban kasa, Bola Tinubu, inda yace masu mulki sun boye Naira don ya fadi zabe.

 

Garba Shehu ya ruwaito Buhari da fadin haka a jawabin da fitar a yau Asabar, 28 ga Junairu, 2023.

 

A cewarsa, attajirai masu boye aka nufi dakilewa ba talaka ba.

 

Ya jaddada cewa sauya fasalin Naira ya zama wajibi saboda dakile masu buga kudin jabu, yan rashawa, yan ta’adda da kuma karfafa tattalin arziki.

 

Ya ce yana sane da wahalar da talakawa ke ciki saboda yan kudaden kashewa da suke ajiyewa a gida, saboda haka zai tabbatar da cewa ya share musu hawaye.

Leave a Reply

%d bloggers like this: