Shugaban kamfanin main a Najeriya NNPC Malam Mele Kyari ya ce babu wanda ya ƙara farashin man fetur a ƙasar.

A jawabin shugaban da yak e mayar da martani dangane da batun da wasu masu dakon mai su ka yi, ya musanta batun da su k ace an ƙara farashin man fetur.

A wani taron masu ruwa da tsaki don tattauna matsalar wahalar mai da ake fuskanta wanda taron  da ya gudana a yau Talata, Malam Mele Kyari ya bayyana wasu matsalaloli da ke kawo cikas wanda aka gaza samar da tsayayyen farashi ga gidajen mai.

Sai dai ya alaƙanta hakan da masu ruwa da tsaki da su ka halarci taron wanda ya ɗora alhakin hakan a wuyansu.

Kuma ya buƙaci su gabatyar da wanda ya ƙara farashin ko kuma hujjar siyan man a farashin da ya ɗara na gwamnati.

A baya dai cikin wata tattaunawa da shugaban masu gidajen mai masu zaman kansu yay i d BBC ya shaida cewar, gwamnatin Najeriya ta ƙara farashin man fetur a hukumance da kashi 8.8.

Leave a Reply

%d bloggers like this: