Rundunar ƴan sanda a ƙasar Pakistan sun tabbatar da mutuwar wasu matasa 49 da su ka rasa rayuwarsu sanadin kifewar kwale-kwale.
Matasan ƴan tsakanin shekaru 7 zuwa 14 sun gamu da ajalinsu a ranar Lahadi yayin da su ke hanya don tafiya a wani ruwa.

Jami’an sun ce matasan dukkansu ɗalibai ne kuma ana cigaba da aikin ceto wasu da ba a gani ba.
Wani cikin ma’aikatan ceton ya tabbatar da cewar an ceto mutane 1122 bayan ninka ayyukan ceto da su ka yi.

Rahotanni sun ce mutanen sun rasu ne a sandin sanyin da ruwan ke da shi kasancewar ana tsaka da tsananin sanyi a ƙasar.

Mai magana da yawun ƴan sandan Fazal Naeem y ace a yau Talata an ske gano wasu mutane biyar ciki har da malami guda ɗaya.
Sai dai y ace bayan bincike an gano cewar hatsarin ya faru a sanadin ɗaukar mutanen da su ka zarce ƙa’ida a kwale-kwalen.