Yayin da babban bankin Najeriya CBN ya amince da ƙara wa’adin kwanaki goma don ci gaba da karɓar tsofaffin kuɗi.

Ƴan najeriya na ci gaba da kokawa dangane da yadda lamarin harkokin kasuwanci ya ƙara tsayawa cak musamman a jihar Kano.
Mutane daban-daban na kokawa a kan rashin wadatattun tsofaffi da sababbin kuɗi, sannan ga dogayen layi a bankunan da ake karɓar sababbin kuɗi wajen na’urar cirar kuɗi ta ATM.

Matashiya TV ta zagaya tare da jin ra’ayin wasu daga cikin mutane a kan ƙarin da akan ƙarin wa’adin da babban bankin ya yi.

Fadar shugaban ƙasa ta tabbatar da cewar wannan tsari da ta fito da shi kuma ta amince da shi, zai taimaka wajen bunƙasa tattalin arziƙi tare da karya alƙadarin masu garkuwa da mutane da masu cin hanci da rashawa
