Kungiyar diallan man fetur a Najeriya IPMAN ta janye wani marni da ta bai wa masu gidajen mai na rufewa saboda wasu dalilai.

Shugaban kungiyar Mohammed Kuluwa ne ya sanar da haka a wata takarda mai sanye da sa hannunsa.
Janyewar ta biyo bayan umarnin da uwar kingiyar ta kasa ta bai wa mambibinta da su dakatar da duk wanii aiki zuwa wani lokaci.

A sanawar janyewar sun bayyana cewar kungiyar na tattaunawa da masu ruwa da tsaki a kan lamarin domin shawo kan matsalar.

A sanarwar farko, kungiyar ta dauki matakin haka ne a kan karanciin man fetur da kuma kokarin tilastasu na siyar da shi a farashin da musu gidajen man za su yi asara.
Mutane na kokawa a kan karancin mai da tsadarsa wanda hakan ya kara ta’azzara tsanani da ake ciki musamman masu. ta’ammali da shi yau da kullum.