Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya buƙaci haɗaɗɗiyar daular larabawa ta ɗage takunkumin hana ƴan Najeriya izinin shiga ƙasar.

 

Shugaban ya miƙa roƙon ne yayin da ya ke yi wa shugaban Sheik Mohamed Bin Zayed Al Nahyan ta’aziyya bias rasuwar ƙanwar mahaifiyarsa.

 

Ta’aziyyar da shugaba Buhari ya miƙa ta wayar salula, kuma daga nanan su ka ci gaba da tattaunawa a kan dangantakar ƙasashen biyu.

 

Shugaba Buhari ya buƙaci sarkin ya da gwamnatinsa su sake duba dokar hana ƴan Najeriya da su ke buƙatar zuwa ƙasar a sake duba dokar hana zuwansu.

 

Sanarwar da mai  Magana da yawunsa Malam Garba Shehu ya fitar a yau, y ace shugaba Buhari hukumomin tsaron ƙasashen biyu za su magance matsalolin da ake fuskanta.

 

Kuma shugaban ya buƙaci kamfanin jiragen sama na Emirates ya koma bakin aikinsa bayan dakatar da jigilar mutane daga Najeriya.

 

 

Leave a Reply

%d bloggers like this: