Hukumar tsaron ta farin kaya (DSS) ta kara tsaurara bincike da nufin kamawa tare da gurfanar da gwamnan babban bankin Najeriya (CBN), Godwin Emefiele a gaban kuliya bisa zargin bada kudaden ta’addanci da zamba.

Hakan dai na zuwa ne a daidai lokacin da aka ce sojoji na baiwa gwamnan babban bankin kasar kariya a gida da kuma ofishi a wani yunkuri na dakile kamun da ake son yi masa, zargin da hedkwatar tsaro ta musanta.
Biyo bayan yunkurin da ta yi a baya na cafke gwamnan koli na bankin, jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa rundunar ‘yan sandan sirri ta sake sabunta bincike kan wasu zarge-zarge da ake yi masa da nufin kama Emefiele da ke gaban kotu domin fuskantar shari’a.

Jaridar Premium Times ta wallafa cewa kwanan nan wasu bayanai na musamman da ya samu daga takardun kotu kan cece-kucen da ake yi na neman Emefiele, ciki har da bayar da tallafin yan bindiga da ba a san su ba da kuma mambobin haramtacciyar kasar Biafra (IPOB).

Gwamnatin tarayya ta haramta kungiyar IPOB mai fafutukar neman ballewa tare da kafa kasar Biafra.
Mambobin kungiyar sun kashe daruruwan fararen hula da jami’an tsaro a cikin ‘yan shekarun da suka gabata tare da kona alamomin hukuma kamar na ‘yan sanda da sojoji, ofisoshin INEC da sauransu.
A cikin rahoton da kafar yada labarai ta yanar gizo ta fitar, an kuma zargi Emefiele da yiwa gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari zagon kasa, da tallafawa ayyukan ta’addanci, da kuma aikata wasu laifukan da suka shafi tattalin arziki da ke da nasaba da zagon kasa ga tsaron kasa Najeriya.
Ta kuma zargi gwamnan CBN da karkatar da reshen CBN, NIRSAL, da kuma shirin Anchor Borrowers Programme na babban bankin.