Gwamnatin tarayyar Najeriya ta bayar da umarnin rufe dukkan iyakokin Najeriya a ci gaba da shirye-shiryen babban zaben kasar wanda zai gudana a gobe Asabar.

 

Hakan na kunshe ne ta cikin wata sanarwa da shugaban hukumar shige da fice ta Najeriya NIS Isa Jere ya fitar a shafin hukumar na Twitter a birnin tarayya Abuja.

 

Jere ya ce za a rufe dukkan iya kokin ne a gobe Asabar da kuma ranar Lahadi 26 ga watan Fabrairun 2023.

 

Shugaban ya bayyana cewa rufewar za ta fara aiki ne da misalin karfe 12 na dare zuwa karfe 12 na daren ranar Lahadi.

 

Jere ya bukaci kwamandojin da ke aikin a dukkan iyakokin kasar da su bi umarnin da aka basu.

 

Isa Jere Ya kara da cewa hukumar ta shirya tsaf domin ganin ta bayar da gudummawa a lokacin babban zaben.

Leave a Reply

%d bloggers like this: