Jami’an rundunar sojin Najeriya sun hallaka ‘yan bindiga biyar da kuma kwato manyan makamai a yankunan birnin Gwari da Chikun a Jihar Kaduna.

Mataimakin daraktan yada labaran runduna ta daya Laftanar-kanar Musa Yahya ya bayyana hakan a ranar Alhamis.

Daraktan ya ce jami’an sojin sun kwato bindiga kirar AK47 tare da abubuwan fashewa harsasai da kuma ababen hawa daga hannun ‘yan bindigar da su ka hallaka.

Kanal Musa ya kara da cewa jami’an nasu sun kuma kwato yankunan Sabon birni zuwa Mando Maidora zuwa Dogon Dawa Saulawa Galadimawa Farin ruwa da kuma Polewire da ke kananan hukumin birnin Gwari da Chikun ta Jihar.

Musa ya ce sun gudanar da aikin ne domin samar da wadataccen tsaro domin gudanar da babbar zaben kasar cikin koshin lafiya.

Kazalika Janar Musa Yahya ya bayyana cewa jami’an sun kwato babura goma wasu da dama kuma su ka kone da bindiga kirar AK47 biyu abubuwan fashewa biyu harsasai da kuma wayoyin hannu guda biyu.

Daraktan ya ce hadin gwiwar runduna ta daya da jami’an sojin sama su ka yiwa ‘yan bindigar ruwan wuta a Jihar ta Kaduna.

Leave a Reply

%d bloggers like this: