Rundunar yan sandan Najeriya reshen Jihar Legas ta musanta labarin da ake yadawa na cewa yan bangar siyasa sun farwa babbar kasuwar Island a yau Litinin.

Mai magana da yawun rundunar yan sandan jihar Legas Benjamin Hundyin shine ya musanta rade radin inda ya ce labarin bai tabbata ba.
Ya ce labarin da ake yaɗawa cewa yan daba sun shiga kasuwar Island tare da lalata shaguna da kuma jiwa mazauna kasuwar raunika.

A safiyar yau ne wasu daga cikin mazauna kasuwar suka isa ofishin hukumar yan sanda da cewa sunji an ce an farma kasuwarsu.

Sai dai kakakin yan sanda Benjamin ya bayyana musu yadda batun yake Kuma kasuwa tana akule kamar yadda aka yi yarjejeniya da yan kasuwar.
Sannan ya ci gaba da cewa jama a su ci gaba da bayar da hadin Kai kamar yadda suke bayarwa yanzu haka kuma su zauna lafiya da junan su har a zuwa fadar sakamakon zabe.