Rundunar yan sandan jihar Ebonyi ta tabbatar da hallaka wani mai rike da sarautar gargajiya a jihar.m

Mai magana da yawun rundunar yan sandan jihar SP Onome shi ne ya bayyana haka ga manenma labarai a yau Talata a Abakalaki.


SP Onome ya ce sun samu sanarwa akan wasu da ake zargin yan bindiga ne sun hallaka mai rike da sauratar gargajiya wato Mr Igboke Emuezeokaha a karamar hukumar Ezza ta kudu a jihar Ibonyi.
Ya ce bisa samun rahoton hakan sun tura Jami ai yankin tare da kwararru domin tabbatar da kamo wadanda suka yi aika aikar.
An dade ana samun yawan asarar rayuka harma wadanda suke wani da mukami a kasa Najeriya a kudancinta da Arewaci.
Matsalar naa neman gagarar gwamnati tsawon shekaru, duk da cewa wasu suna cire tsammani akan hakan.