Kwamitin kamfen yakin neman shugaban kasa na jam’iyyar adawa ta PDP ya yi kira ga hukumar shirya zabe ta kasa mai zaman kanta ta soke dukkan sakamakon da aka sanar kawo yanzu.

 

Mai magana da yawun kamfen, Daniel Bwala ya bayyana hakan a jawabin da ya fitar yau Talata.

 

Ya ce adakatar da tattara zaben yanzu kuma a bada amsa game da korafe-korafen da jam’iyyu sukayi game da kin amfani da na’urar BVAS da sauya sakamako a yanar gizo.

 

Ya kara da cewa a zabi sabon ranar gudanar da zabe a wadannan wurare kuma a tabattar da cewa an daura sakamakon, wajibi ne a yi amfani da BVAS kan a ce anyi zabe na gaskiya.

 

Ayi watsi da dukkan sakamakon da aka sanar har zuwa lokacin da aka daura dukkan sakamako daga runfunan zabe zuwa yanar gizon INEC, kuma a sanar da su, kuma a baiwa wakilun jam’iyyu nasu kwafin.

Leave a Reply

%d bloggers like this: