Hukumar kashe gobara a jihar Kano ta tabbaatar da tashin gobara a babbar kasuwar Kurmi ta jihar Kano.

Mai magana da yawun hukumar Saminu Yusif ne ya shaida haka a wata sanarwa da ya aikewa manema labarai.
Ya ce bayan sun karɓi kiran waya daga wani mai suna Aliyu A Alkasim, jami’ansu sun je kasuwar da asubahin yau Laraba.

Ya ce sun aike da kiran ga sauran ofisoshinsu na tsakiyar birni domin kai daukin gaggawa.

Aƙalla shaguna shida da kuma waasu rumfuna guda 74.
Sai dai ya ce babu asarar rai ko jin rauni.
Sannan su na ci gaba da bincike don gano dalilin tashin gobarar.