Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya taya zaɓaɓɓen shugaban ƙasar Najeriya Bola Tinubu murnar zama sabon shugaba.

Muhammadu Buhari wanda ya ayyana Bola Tinubu a matsayin wanda ya fi dacewa da mulkin kasar.

Sannan ya misalta zaben da aka gudanar a matsayin ingantacce kuma sahihin zaɓe.

Sannan ya shawarci jam’iyyun da su ka yi rashin nasara da su je kotu domin gabatar da kokensu.

Wasu daga cikin jam’iyyun da su ka shiga zaɓen sun yi watsi da sakamakon tare da zargin magudi a zaben.

Tuni aka mika sakamakon cin zaben shugaban kasar ga zaɓaɓɓen shugaban da mataimakinsa wanda shugaban hukumar zaben INEC ta kasa farfesa Mahmud Yakubu ya miƙa musu.

Leave a Reply

%d bloggers like this: