Rahotanni da ke yawo a yanzu na nuni da cewar babban bankin Najeriya CBN ya halasta amfani da naira 200, 500, da kuma nairaa 1,000 har zuwa ƙarshen watan Disamba.

Hakan na kunshe a qata sanarwa da bankin ya wallafa mai duake da sa hannun daraktan sadarwa na bankin Isa Abdulmumin.

Bankin ya sanar da cewa akwai halascin amfani da tsaffin kudin da aka sauyawa fasali har zuwa ranar 31 ga watan Disamban Shekarar da mu ke ciki.

Bankin ya sanar da cewar ya bi umarnin kotu da ta yanke hukunci fiye da mako guda da ya gabata.

Sai dai duk da haka bankin bai bayar da umarnin ci gaba da amfani da tsaffin kudin ba sai a sanarwar da su ka sanar yau Litinin.

Tun tuni ake ta kai kawo wajen bin umarnin kotun wadda ta yi hukunci fiye da mako guda da ya gabata.

 

Leave a Reply

%d bloggers like this: