Mataimakin gwamnan Kano kuma ɗan takarar gwamna a Kano Nasiru Gawuna ya jajantawa waɗanda ibtilain gobara ya smau a kasuwar singa ta Kano.

Dakta Nasiru Yusif Gawuna wanda ya bayyana alhininsa ta bakin babban sakataren yaɗa labaransa Hassan Musa Fagge.
Ya kuma yi jaje ga waɗanda gobarar ya shafa ya na mai cewar lamarin abin takaici ne matuƙa.

Dakta Nasiru Yusif Gawuna ya miƙa sakon jajen a madadin ɗan takarar mataimakinsa Hon. Murtala Sule Garo.

Sannna ya yabawa hukumar kashe gobara ta jihar Kano bisa ƙoƙarin ganin sun shawo kan lamarin.