Hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa NDLEA ta bayyana cewa ta kama wani sarkin gargajiya da kuma tubabben dan boko haram da ake zargi da safarar miyagun kwayoyi.

A cikin sakon da ta wallafa a shafin ta na twitter ta ce ta kama mutanen hadi da wasu mutane 35 wadanda su kayi yunkurin safarar miyagun kwayoyi a cikin firji a filin sauka da tashi na Murtala Muhammad dake jihar Legas kamar yadda mai magana da yawun hukumar Femi Babafemi ya wallafa.


Basaren gargajiyar mai suna Bala Akinkola Adebayo Sarkin Kajola a garin dake kan iyaka da jihohin Edo da Ondo ana zargin sa da safarar kwayoyi da nauyin su ya kai tan 2.2 a fadin jihohi 12.
Sannan hukumar ta ce ta kama Alayi Modu wanda ya kwashe shekaru 15 yana cikin yan boko haram kafin ya mika wuya, sannan ya ci gaba da safarar kwaya.
Shugaban hukumar Janar Buba Marwa mai ritaya ya jinjinawa jami’an hukumar a fadin kasa Najeriiya bisa irin namijin kokarin da ya ce sun yi wajen kamen masu aikata miyagun laifi a kasa.
Har yanzu dai ana lissafa kasa Najeriya a matsayin kasar da take fama da ta’amali da miyagun kwayoyi a duniya duk da masana na cewa nan bada jimawa baza a magance matsalar a Najeriya.