Dan takarar shugaban kasa a jamiyar Labour Party woto Peter Obi ya bayyana dalilin da ya sa yake kalubalandantar hukummar zabe ta kasa INEC a kotu.

Obi ya ce ya na kalubalantar INEC akan yadda ta bi wajen ayyana nasarar Bola Ahmad Tunubu a matsayin wanda ya lashe zabe.
Dan takarar ya bayyana hakane a yau Litinin cikin wata hira da aka yi da shii da shi da gidan talabijiin na chennels da safe.

Peter OBi ya ce ba yana musun nasara da Bola tunubu ya samu bane a a illa hanayar bayyana sakamakon da ce da akabi aka fada bai yarda da ita ba.

Domin zababben shugaban kasa Bola Ahmmad Tunuubu uba ne a gareshi ya na mai girmama shi a ko da yaushe.
Peter Obi ya ce suna so su gina Najeriya ne kamar sabuwa kuma dole
hakan bazan yiwa sai an hada karfi da karfe a yayin aikin.
A ranar 25 ga watan fabarairun da ya gabata ne aka gudanar da zaben shugaban kasa da yan majalissun tarayya inda hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC ta ayyana dan takarar jamyiiyar APC bola Ahmad Tunubu a matsayin wanda ya lashe zabe a Najeriya da kuri a mafi rinjaye.
Rundunar yan sandan jihar Ogun ta tabbatar da kubutar da wani dan jarida da aka yi garkuwa shi a makon da ya gabata wato Seun Oduneye.
An yi garkuwa da shi a ranar Alhamis din da ta gabata ne a yayin da yake kan hanyar zuwa Ijebu Ode daga Abekuta a cikin motarsa kirar Toyota.
An rawaito cewa an yi garkuwa da dan jaridar ne da misalin karfe 7;50 na yamma a mota sai yan bindiga suka bude masa wuta tare da tsayar da shi.
Sai dai kamar yadda majiya ta bayyana yan garkuwa sun nami matarsa a waya domin biyan naira miliyan 30 don fansar mijinta.
Mai magana da yawun rundunar yan sandan jihar Abimbola Oyeyemi a yau Litiinin ya bayyana cewa dan jarida Oduneye ya shaki iskasar yanci.
Oyeyemi ya ce bayan aiki da kwararru ba wadanda suka shiga dajin ba dare ba rana don ganin an kubutar da wanda aka yi garkuwa shi kuma an yi nasara.
Ya ci gaba da cewa lokacin da jami an yan sandan suka shiga dajin sun yi artabu da yan bindigan tsawon mintuna 45 ana fafatawa sai dai da suka ji ba da ma suka tsere da muggan raunuka a jiki.
Sannan suka jefar da wanda suka yi garkuwar da shi tare da rauni a jika.
Bayan sammun nasara Kwamishinan yan sandan jihar Frank Mba ya yabawa jami’an tare da jinjina musu bisa wanannan aiki da suka yi mai kyau.
Daga karshe CP Frank Mba ya ce yana mai rokon duk wanda ya samu rauni a yayin fafatawar da aiki tsakanin yan sanda da yan bindiga a kauyen yayi saurin sanarwa.
Ya ce yan bindiga su bar jihar Ogun don kuwa sun shirya yaki da su.