Rundunar ‘yan sandan jihar Cross Rivers ta tabbatar da gano gawar Farfesa Felix Akpan na Jami’ar Calabar (UNICAL).

 

Kakakin Rundunar ’Yan sandan Jihar, SP Irene Ugbo, wanda ya tabbatar da faruwar lamarin, ya ce an gano gawar ne a ranar Lahadin da ta gabata tare da harbe-harbe a wurare da dama a gidansa da ke Lamba 181, Duke Town Close.

 

Mista Ugbo ya ce sun fara kama waɗanda ake zargi da hannu yayin da jami’ai suka buɗe shafin bincike kan kisan.

 

Akwai wanda ake zargi tsare a hannun su, wanda ya yi ikirarin abokin mamacin ne, ya ce bai san abinda ya faru ba ko wanda ya soka masa wuka har ya mutu.

 

Wata majiya da ta nemi a sakaya sunanta, ta ce mamacin, tsohon shugaban sashen kula da jin daɗin daliban jami’ar UNICAL ya yi wani baƙo ranar Asabar.

 

Baƙon ya tafi da sanyin safiyar ranar Lahadi zuwa Akampka kafin daga bisani a gano gawar farfesan.

 

Leave a Reply

%d bloggers like this: