Gwamnatin ƙasar Amurka ta sake miƙa buƙata ga shugaba Buhari don ganin ya janye tallafin man fetur kafin karewar wa’adin mulkinsa.

Yayin da ya rage ƙasa da kwanaki saba’in wa’adin gwamnatinsa ta ƙare.


Ambasadar ƙasar Amurka a Najeriya Mary Beth Leonard ta ce yaa kamataa shugaba Buhari ya kammala aikin cire tallafin man kaafin fita daga ofishinsa.
Tun a baya, gwamnatin kasar ta bukaci shugaba Buhari ya cire tallaafin maan fetur, wanda wasu gwamnonin kasaar su kaa dade da jan hankalinsa a kai.
Ambasadar ta tabbatar da cewar, gwamnatin Amurka za ta ci gaba da bai wa Najeriya dukkanin taimakon d ata buƙata a ɓangaren lafiya.
Ambasar na gab da kammala aikinta tare tare da komawa kasar yayin da shugaba Buhari ke kokarin miƙa mulki ga zaɓaɓɓen shugaban ƙasar Bola Ahmed Tinubu.