Jam’iyyar NNPP ta sanar da dakatar da zanga-zangar da ta shirya yi don nuna goyon baya ga hukumar zabe mai zaman kanta INEC a jihar Kano.

Tun da fari dai a cikin wata wasika da jam’iyyar ta aikewa da kwamishinan ‘yan sandan jihar kano, mai dauke da sa hannun shugabanta na jiha Umar Haruna Doguwa, NNPP ta ce zanga-zangar ta goyon bayan INEC ce akan zanga-zangar jam’iyyar APC.

Jam’iyyar ta NNPP ta shirya haduwa ne daga duk-kan kananan hukumomi 44 kana su wuce filin Dalar Gyada domin tafiya helikwatar hukumar INEC a ranar alhamis.

sai dai lokacin da manema labarai suka tuntubi kakaKin zabebben gwamnan jihar Kano, Sunusi Bature Dawakin Tofa, ya ce sun dage gudanar da zanga-zangar daga yau alhamis har zuwa nan gaba sai dai bai bayyana ranar ba.

An rawaito yadda wasu kusoshin jam’iyyar APC mai mulkin jihar suka gudanar da zanga-zanga a ofishin hukumar zabe na jihar Kano kan yadda hukumar ta ayyana jam’iyyar NNPP a matsayin jam’iyyar da ta lashe zaben gwamna da aka gudanar a jihar.

Leave a Reply

%d bloggers like this: