Hukumar zabe mai zaman kanta a Najeriya INEC ta sanar da cewar za a bayar da takardar shaidar lashe zaɓen gwamnonin Najeriya 26 daga cikin 36.

A wata sanarwa da kwamishinan zaɓe na ƙasa kumaa shugaban wayar da kan masu zaɓe ya sanyawa hannu, Sanarwar ta ce jihohi 26 ne kaɗai aka kammala zaɓe kuma aka ayyana ƴan takarar da za a ba su sakamakon lashe zaɓen.

Hukumar ta ayyana ranakun 29 da 30 da kuma ranar 31 gaa watan da mu ke ciki domin miƙa sakamakon lashe zaɓen ga gwamnonin.

Haka kuma hukumar ta ce an kammala zaɓen sanatoci 104, da ƴan majalisar wakilai 392 da ƴan majalisar dokokin jihohi 935 ne du ka kammala.

Sai dai hukumar ba ta zayyano sunayen takwas daga jihohin da za a yi zaben cike gurbin ba illa jihohin Adamawa da Kebbi.

A jihar Kano ana ta tantama dangane da kammaluwar zaɓen ko akasin haka, wanda hukumar har yanzu ba ta magantu a kai ba.

Idan za ku iya tunawa mai magana da yawun zaɓaɓɓen gwamnan Kano Sanusi Bature Dawakin Tofa ya faɗa cewar, za a bai wa zaɓaɓɓen gwamnan shaidar lashe zabe a ranar Laraba.

 

Leave a Reply

%d bloggers like this: