Kaftin din kungiyar kwallon kafa ta kasa Najeriya wato Ahmad Musa ya kafa irin tarihin da dan wasan faransa ya taba kafawa Zinedin Zidene na yawan fafatawa kasar sa wasan tamola.

kamar yadda tarihi ya nuna Musa ya kafa tarihin yawan bugawa Najeriya wasa har sau 108 a duniya farawa daga shekarar 2010.
Ana lissafa cewa tsohon dan wasan faransa wnda ya taka rawar gani a sha’anin buga kwallo da kuma horaswa ya fafata wasanni 108 a duniyarsa ta kwallo kamar dai Ahmad Musa na Najeriya ya yi.

Sannan Ahmad Musa ya zarta yan wasa kamar Patrick Vieira da kuma Lampard wajen fafata wasa a matakin kasa.

Ahmad musa dai ya kafa wannan tarihi ne bayan fafata wasa da aka yi a jiya Litinin tsakanin kasa Najeriya da kuma kasar Guinea da ci 1-0
Sannan Ahmad Musa tun da daga shekarar 2010 da ya fara wasa ya zurawa Najeriya kwallaye 16 kuma shine ya fi kowanne dan wasan Najeriya kwallaye a raga a gasar cin kofin duniya da kwallo hudu.
kuma ya ci kwallaye 92 a kungiyoyi daban-daban na duniya.