Akalla mutane 784 ne suka kamu da cutar zazzabin lasa tare da hallaka mutane 142 a farkon shekarar 2023 da muke ciki.

Hukumar dake yaki da cututtuka masu yaduwa a Najeriya NCDC ita ce ta bayyana cewa mutane 142 suka mutu a yayin da 784 su ka kamu da cutar.

A rahoton NCDC ta ce cikin makonni 11 ne aka samu rasuwar mutane 142 da kamuwar 784 a shekarar 2023.

Adadin da ya nuna mutane 3,826 ne ke dauke da cutar a gabadaya kasar tun bayan barkewarta a kasa Najeriya.

kuma cutar zazzabin lasa ta fi kamari ga masu shekaru 21 zuwa 30 a kasar.

Kamar yadda hukumar NCDC take bayyanawa ta ce cutar ta yawaita a kasashen yammacin afrika kamar Mali Benin, Ghana, Togo, Laberiya, Najeriya da dai sauransu.

Sannan ta yi kamari a jihohin Najeriya kamar Edo, Ondo, Ebonyi, Bauchi, Benue, Ribas, Taraba, Filato da jihar Nasarawa.

Daga karshe NCDC ta ce mutane su dinga lura da kayan da za su dinga amfani da su domin kaucewa abin da ya shafi bera.

Leave a Reply

%d bloggers like this: