Zaɓaɓɓen shugaban ƙasar Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya tabbatarwa da yan Najeriya cewar ba zai sauka daga tanadin da ya yi wa kasar ba.

Bola Tinubu ya ce mafarki ne da ya daɗe a zuciyarsa kuma yaake son tabbatar da shi a zahiri.
A wani sako da ya aike, sakamakon zagayowar ranar haihuwarsa, ya ce ba zai saba daga alkawuran da ya daukarwa yan Najeriya ba yayin yakin neman zabe.

Hakan na zuwa ne mako guda, bayan sanar da cewar shugaban zai ziyarci kasashen Habasha, Faransa da saudiyya.

Ya ce bayan kaddamar daa shi da zai fara aiwatar da kudirin da ya daukarwa yan Najeriya.
Shugaban ya cika shekaru 71 a duniya, wanda ya sadaukar da ranar haihuwarsa domin tunawa da nauyin da ya daukarwa yan Najeriya.