Hukumar tsaron farin kaya ta DSS a Najeriya ta ce ta gano shirin wasu yan siyasa na haifar da fitina don hana miƙa mulki ga zaɓaɓɓen shigaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu.

Mai magana da yawun hukumar Peter Afunanya ne ya sanar da haka a wata sanarwa da ya saanyawa hannu yau Laraba.
Ya ce sun gano shirin yan siyasar na yunkurin tayar da fitina mai ƙarfi a kasar yadda za a sanya dokar ta ɓaci.

Ya ce shirin hakan sun yi me da nufin hana miƙa mulki ga zaɓaɓɓen shugaban ƙasar Bola Ahmed Tinubu.

Hukumar ta yi gargadi cewar shirin da ake
na iya kai wa ga kazamin rikici a Najeriya.
Haka kuma rikicin na iya shafar dukkanin zababbun shugabannin da za su kama aiki a karshen watan Mayun shekarar da mu ke ciki.
Akwai wasu manyan jihohi da yan siyasar ke shirin haddasa zanga-zanga wanda kuma za na iya kai wa ga kazamin rikici a Najeriya.
Haka kuma rikicin na iya shafar dukkanin zababbun shugabannin da za su kama aiki a karshen watan Mayun shekarar da mu ke ciki.