Dan takarar shugabancin kasa karkashin jam’iyyar NNPP Engr. Rabi’u Kwankwaso ya musanta zargin da ake yimasa na cewa bazai bar gwamnan jihar mai jihar gado Engr. Abba Kabir Yusuf ya gudanar da gwamnatinsa ba, ba tare ya yimasa katsa landan ba.

Kwankwaso ya bayyana cewa bashi da shirin yiwa sabuwar gwamnatin katsalandan a cikin ayyukanta.

Tsohon gwaman na kano na bayyana haka ne a lokacin da yake tattaunawa da manema labarai a birnin kano.

Kwankwaso ya kara da cewa akwai abubuwa da zai bada shawara kana akwai wuraren da zai bari sabuwar gwamnatin tayi aikinta kamar yadda doka ta tanada.

Rabi’u kwanwakso wanda shohon Ministan tsaro ne ya tabbatar da cewa yana da yakinin cewa sabuwar gwamnatin zatayi amfani da shawararsa.

Leave a Reply

%d bloggers like this: