Hukumar kiyaye faruwar hadura ta kasa reshen jihar Bauchi ta tabbatar da mutuwar mutane biyar da suka kone kurmus a wani hadarin mota akan babbar hanyar Bauchi zuwa jos.

Hukumar ta ce hadarin ya farune bayan da wata mota kirar Toyota tayi tawo mu gama da wata motar kirar Peugeot wadda ke dauke da fashinjoji a cikinsu bayan da motar ta ku6ucewa daya daga cikin direbobin.
An rawaito cewa maza biyar da ke cikin motar sun mutu bayan da ta kone kurmus, yayin da motar ta kama da wuta.

Hukumar ta bayyana cewa an mika mutanen tare da motocin ga hukumar ‘yan sanda shiyyar Toro da ke jihar ta Bauchi.
