Yan sanda sun kama wani matashi da ake zargi da yiwa jaririya ‘yar wata tara fyade a jihar Legas.

Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar SP Benjamin Hundeyin shine ya tabbatar da faruwar al’amarin.
Kakakin ya bayyana cewa wani mutum ne ya kaiwa jami’ansu korafin aikata fyade tun a ranar Litinin.

Ya kara da cewa wanda ake zargi ya shiga gidan mahaifiyar jaririyar ne a inda anan ne ake zargin yayiwa jaririyar fyade.

Benjamin ya kara da cewa mahaifiyar jaririyar ta je ofishin ‘yan sanda a inda aka bata takardar da zata bada dama a duba lafiyar ‘yar tata.
Kakarin ‘yan sandan na jihar Legas ya tabbatar da cewa wanda ake zargin ya amsa laifinsa zakuma a gabatar dashi a gaban kotu domin ya girbi abin da ya shuka.