kungiya gwamnonin Najeiya ta yi Allah wadai da kalaman da wasu suke yi akan cewa ana yunkurin kafa gwamnatin rikon kwarya kafin rantsar da sabbin gwamnonin da aka zaba.

Shugaban kungiyar gwamnonin na kasa gwamnan jihar Sokoto Aminu Waziri Tamabuwal shi ne ya bayyana haka ga manema labarai inda ya ce suna tir da wannan batun.
Tambuwal ya ce an jiyo wasu suna bayyana cewa za a kafa gwamnatn rikon kwarya a jihohin bayan zaben da aka gudanar a ranar 18 ga wata don haka hakan fa ba zai yiwa ba.

Ya ce za su kare martabar damakwaradiyyar Najeriya kamar yadda take, kafa wata gwmnati ta rikon kwarya zai haifar da rudani a kasar nan.

Ya ce za su yi duk mai yiwa wajen tabbatar da kare manufar damakwaradiyya.
Sai dai a cikin bayanan sa bai bayyana sunayen wadanda suka yi wannan ikirarin ba amma ya ce hukumar tsaron farin kaya ta DSS ta yi duk mai yiwa wajen ta kama wadanda suke da wannan manufar a hukumance.
Duk da cewa cikin zaben da akai akwai kura kurai amma za su ci gaba da kare martabar dama kwaradiyya a kasar a cewar tamabuwal.