Kungiyar Kwadago ta TUC ta gargadi gwamantin tarayyar Najeriya kan cire talafin man Fetur a matsin rayuwar da ake fama da shi.

Mai magana da yawun kungiyar TUC na kasa Aminu Toro shi ne ya bayyana haka ga manema labarai inda ya ce hakan zai jefa rayuwar talakawan Najeriya mawuyacin hali.

Ya ce gwamnati ta sha bayyanawa cewa mutane Najeriya na fama da talauci da tsadar rayuwa, don haka indai aka cire tallafin man fetur sauran kayan masurufi za su iyayin tsada a kasar.

Kuma su kungiyar su ba za ta yarda da wannan tsarin ba a hukumance kamar yadda Toro ya ke cewa ba a taba cire tallafin fetur ba har sai an zauna da hukumomi da kuma masana don ganin yadda lamarin zai tafi.

Daga karshe ya ce cire wannan tallafi ba shi ne mafita ba ga yan Najeriya a samo musu hanyar da za ta saukaka musu kayan masarufi shi ne ya fi.

Leave a Reply

%d bloggers like this: