Wasu da ake zagi yan bindiga ne sun hallaka mutane 15 a garin baka karamar hukumar Ardo ta jihar Taraba.

yan bindiga wadanda da suka je yankin da yawansu kusan 60 sun dinga harbiin jama a ba kakkautawa.
Wani dan asalin garin mai suna garba ya bayyana cewa yan bindiga sun je kauyen su da misalin karfe 7;30 na dare yayin da jama a suke gudanar da sallar tarawi.

an jiyo harbin bindiga kan mai uwa da wabi inda aka hallaka mutane da dama wasu ma ba a gansu ba.

ya ce yanzu haka an binne mutane goma inda ake ci gaba da nemo wasu da dama.
sannan ya ce yan bindigan sun kore shanun mutane tare da kone gidaje lokacin da suka zo.
Sai dai da aka tuntubi rundunar yan sanda busu bayyana mutanen da suka mutu har ya zuwa yanzu ba.