Zababben Gwamna jihar Kano mai jiran gado wato Abba kabir Yusif ya shawarci masu bai wa gwamnatin kano bashi su dakata haka har zuwa ranar 29 ga watan mayu wato ranar rantsuwa.

A karshen makon da mu ka yi bankwana da shi ne aka jiyo Abba Gida-Gida ya na cewa masu yin gine-gine da siyan filayen gwamnati su dakata da yin hakan.

Batun da ya sa gwamnatin jihar kano ta ce har yanzu Ganduje shi ne gwmanan don haka Abba ba shi da hurumi har sai ya hau karagar mulki a hukumance kamar yadda kwamishnan yada labarai na jihar Muhammad Garba ya bayyana.

Sai dai an sake jiyo sabon gwamna mai jiran gado Abba gida Gida ya na cewa masu bai wa gwamnatin kano bashi an shawarce su daina don kuwa duk bashin da bai cike kai idoji ba gwamnati ba zata yi lakari da shi ba.

Sannan zai zurfafa binciike akan basussukan da ake bin gwamnatin don tabbatar da gaskiyar lamarin yadda aka karbi bashin.

Leave a Reply

%d bloggers like this: