Hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi a jihar Filato ta ce fiye da mutane 240,000 ne ke ta’ammali da miyagun kwayoyi a jihar.

Kwamadan hukumar a jihar Mustapha Umar ne ya bayyana haka wanda y ace adadin mutanen kashi 11 cikin ɗari ne ta’ammali da kayan maye.
Kuma ya ce kashi 11 da ke ta’ammali da kayan ya ƙunshi nasu siyarwa da masu safararsu.

Sannan mutane da ke tsakanin shekaru 16 zuwa 64 ne su ka fi ta’ammali da kayan mayen.

Ya ce ƙaruwar masu ta’ammali da kayan maayen barazana ce ga babba domin hakana na da alaƙa da aikata miyagun laifuka.
Sai dai hukumar na samun nasarar kama masu shan kayan mayen da kuma kama kayan mayen masu yawa wanda ya bayyana haka a matsayin babbar nasarar daƙile dabi’ar a jihar.