Hukumar hanasha da fataucin miyagun kwayoyi NDLEA ta tabbatar da cewa ta kwace tan 2.1 tare da kama mutum 352 da ake zargi da dillancin kwayoyi a jihar Kano.

Kwamandan hukumar na jihar Kano Abubakar Idris Ahmad shine ya bayyana haka yayin wata zantawa da kamfanin dillancin labarai na kasa NAN a yau alhamis.

Ya bayyana cewa sunyi kamen ne daga watan Janairu zuwa Maris da ya gabata.

A cewarsa daga cikin mutane 208 maza ne yayin da 44 suka kasance mata.

ya kara da cewa kwayoyin da su ka kama sun hada da Kilogram 955.3 na tabar wiwi, da Kilogram 1,225 na Kodin da Tramadol, sauran kwayoyin sun hada da giram 25 na hodar iblis.

Sai dai kwamandan ya ce babban kalubalen da hukumar ke fuskanta a jihar shine na shawo kan all’umma domin baiwa jami’an hukumar bayanan sirri, domin kawo karshen ta’ammali da miyagun kwayoyi a fadin jihar.

 

 

 

 

 

Leave a Reply

%d bloggers like this: