Akalla yan gudun hijira 34 ne ake zargin an hallaka a yayin da suke matsuguninsu a jihar Benue.

Lamarin ya faru ne jiya Juma a da misalin karfe tara na dare a karamar hukumar Guma cikin makarantar firamari ta Mgban.
Wani mutum mazaunin garin da abu ya faru a gabansa mai suna Jonah ya bayyana cewa maharan sun je ne da misalin karfe tara na dare a jiya juma a.

A harin an hallaka wata mai ciki da danta inda suka kuma hallaka mutane da dama da kuma jiwa wasu raunuka.

Shima mai bada shawara a fanin tsaro a karamar hukumar ta Guma Christopher Waku ya bayyana yan ta’adan sun hallaka mutane akalla 34 da yi wa 40 daga cikin yan gudun hijirar rauni.
Waku yayin da yake bayyana yadda lamarin ya faru ya ce an samu dayawa daga cikin gawarwakin a cikin ajujuwa.
ya ciki gaba da cewa an samu gawarwaki 24 yanzu haka a cikin aji inda aka samu goma akan titi suna kokarin guduwa su tsira da ransu aka hallaka su.
A banagaren rundunar yan sanda ta bakin mai magana da yawunta ya tabbatar da faruwar lamarin inda ya ce ana ci gaba da bincike a kai.