Gwamnati jihar Bauchi da ta shirya mukabala da babban malamin addinin musulunci Sheik Idiris Abdulaziz dutsen Tanshi da wasu

malaman jihar ta dage zaman zuwa wani lokaci.
Sanarwa dage zaman ta fito daga hukumar shari’ar musulunci ta bakin shugabanta mustapha Illelah sa oi kadan kafin gudanar da zaman a yau.

Tun farko dai ana zargin malam Idiris da wani kalami na cewa ba neman taimako a wurin annabi sai a wurin Allah.

Abun da ya sanya maganar ta kawo ce-ce-ku–ce musammanm a kafar sada zumunta a Arewacin Najeriya.

ganin yadda malamai su ke raddi game da matsalar gwamnati ta shirya gudanar da mukabala da Malam Abdulaziz Idiris Bauchi a yau Asabar.

Sai dai a safiyar yau Asabar ne hukumar shari a a ta jihar Bauchin ta dage zaman.

Mustapha ya ci gaba da cewa kuma an dage zaman ne ba don wani ba a an yi hakanne don dukkansu malaman su shiryawa zaman dama ita hukumar shari’ar.

Daga karshe shugaban hukumar Shari a ta jihar Bauchi Mustapha Baba Illelah ya ce zaman za a yi ba irin zaman titi ba ne shiyasa ake bukatar malamai masana a bangaren da za a tattauna su bayyana sannan da bayar da kariya ga su malaman da za a yi zaman da su.

Leave a Reply

%d bloggers like this: