Wasu da ake zargin masu garkuwa da mutane sun yi garkuwa da akalla mutane 100 a jihar Zamafara.

Kamar yadda BBC ta rawaito ta ce lamarin ya faru ne a kauyen Wanzamai karamar hukumar Tsafe ta jihar Zamafara a jiya Juma a.

Wani mutumin garin ya bayyana cewa Lamarin ya faru ne yayin da yan bindigar suka ritsa wadanda suka yi garkuwa da su a cikin daji bayan sun je diban itace wadanda galibinsu matasa ne yan kasa da shekaru 20 maza da mata.

Ya ci gaba da cewa lamarin ya zama ruwan dare tun da ya shafi kowa a garin in ba a dauki danka ba to za a dauki dan uwanka, akalla masu garkuwan sun dauki matasan 80 zuwa 100.

Wata mata itama da aka dauki yarta ta bayyana cewa yarinyarta ta tafi daji ne domin daukar ice wanda har yanzu ba a ga dawowarta ba.

Sannan suna cikin iftilai tun da yaran suna cikin dajin hannun miyagu ba a san halin da suke ciki ba kamar yadda uwa daga cikin yaran ta bayyana.

kuma har yanzu babu wata alama daga masu garkuwa ko kiran waya.

jihar zamfara ta na cikin jihohin Arewcin Najeriya wadda ke ci gaba da fama da matsalar yan garkuwda mutune dama yan fashin daji kamar yadda Arawacin kasar Najeriya ke fama da wannan matsalar ta rashin tsaro a kasar.

Leave a Reply

%d bloggers like this: